An soki WHO da sakaci kan Ebola

Ebola Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ebola

Wani rahoto a kan bullar cutar Ebola a yankin yammacin Afrika ya soki hukumar lafiya ta duniya WHO kan jan kafa game da al'amuran lafiya.

Rahoton ya gano cewar martanin hukumar ta WHO din ya samu cikas ne sakamakon rashin kudi da kuma rashin kyawon hanyoyin sadarwa tare da hukumomin MDD.

Ya kuma yi kira da a gaggauta yiwa hukumar tankade da rairaya.

Amma kuma ta wani gefen rahoton ya yaba mata wajen taka muhimmiyar rawa a yukurin gano sabbin magungunan kwayar cutar ta Ebola.

A martaninta Hukumar ta WHO ta ce ta amince cewar dole ne a hada cibiyoyinta wuri guda yadda ya kamata domin tinkarar lamuran gaggawa na gaba.

Yanzu haka dai annobar cutar Ebolar ta hallaka mutane fiye da dubu goma sha daya a yankin Afirka ta Yamma--akasari kuma a kasashen Guinea da Saliyo da Liberia ne.