'Yan sanda sun kona wata a Indiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda a Indiya

Wata mata ta mutu a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya bayan da ta yi zargin cewar 'yan sanda biyu sun kona ta a wani caji ofis saboda ta ki bayar da cin hanci.

Kafin ta mutu Neetu Dwivedi mai shekaru 40, ta gayawa kotun majistire cewar 'yan sanda sun bukaci ta basu rupee dubu 100 kwatankwancin dala dubu 1,578.

Ta je ofishin 'yan sandan ne domin a sako mijinta da ake tsare da shi saboda tuhumar sa da ake yi da wani laifi.

Sai dai 'yan sanda sun musanta laifin da ake zargin su da shi kuma sun ce ta yi kokarin kashe kanta ne ta hanyar cinnawa kanta wuta.

An dakatar da 'yan sandan daga aiki kuma babban Minista Akhilesh Yadav ya ba da umarnin ayi bincike a kan lamarin.