EFCC ta damke Nyako da Ohakim

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Efcc na zargin tsofaffin gwamnoni da wawure kudaden al'umma

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin aziki zagon kasa a Nigeria, EFCC ta damke tsofaffin gwamnonin jihar Adamawa da kuma Imo bisa zarginsu da cin hanci da rashawa.

EFCC ta kama Murtala Nyako, tsohon gwamnan jihar Adamawa da kuma Ikedi Ohakim tsohon gwamnan jihar Imo a ranar Laraba.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwajuren, ya tabbatarwa BBC cewa za su gurfanar da tsofaffin gwamnonin gaban kuliya domin su amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake musu.

Hakan na zuwa ne kwana guda, bayan da EFCC din ta damke tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da 'ya'yansa bisa zarginsu da sama-da-fa?i da makuden kudade a lokacin mulkinsa.

Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa a kasar mai arzikin man fetur wacce talauci ya yi wa jama'arta katutu.

Wasu na zargin cewar ayyukan na EFCC na da nasaba da siyasa, zargin da ta musanta.