EFCC za ta kai Sule Lamido kotu

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan da 'ya'yansa sun yi cuwa-cuwar sama da N1.3 bn

Hukumarda ke yaƙi da masu yi wa tattalin aziki zagon ƙasa a Najeriya, EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa tare da 'ya'yansa biyu a gaban kuliya ranar Laraba ko Alhamis bayan ta kama shi ranar Talata.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwajuren, ya tabbatarwa BBC cewa za a kai tsohon gwamnan kotu ne bisa zargin sama-da-faɗi da makuden kudade a lokacin mulkinsa.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan da 'ya'yansa sun yi cuwa-cuwar sama da N1.3 bn.

Ko da a karshen shekarar 2012 jami'an hukumar EFCC sun kama ɗaya daga cikin 'ya 'yan tsohon gwamnan, Aminu Sule yana shirin fita kasar waje da maƙuden kuɗaɗe.