Lauyoyi suna yajin aiki a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ghana na fama da matsalolin tattalin arziki shi ya sa take tsuke-bakin-aljihu.

Lauyoyi kimanin 150 daga dukkanin jihohin kasar Ghana sun fara yajin aiki ranar Laraba.

Lauyoyin na yajin aikin ne domin su matsa lamba kan gwamnati ta kara musu albashi, sannan ta sanya su a cikin tsarin karbar fansho.

Yajin aikin zai kawo tsaiko a kan shari'ar manyan laifuka da ake gudanarwa a kasar.

Kasar Ghana na fama da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya sa take daukar matakan tsuke-bakin-aljihu.