Sarki Sanusi ya 'yantar da Fursunoni 45

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Sanusi na biyu ya bukaci mutane su kyautata hallayarsu

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya 'yantar da Fursunoni kusan 45 bayan da ya biya musu tara da kuma basukan da ke kansu.

A wannan makon ne Sarkin ya biya wa Fursunonin sama da naira miliyan bakwai domin samun 'yanci da kuma walwala, bayan da aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari na wasu lokuta.

Fursinonin da aka 'yantar sun yi zaman gidan-kaso ne a kurkukun Goron Dutse da na Kurmawa a jihar Kano.

Sarki Sanusi ya ce ya ziyarci gidan yarin ne domin kwadaitar da sauran Musulmi su kusanci Ubangiji a daidai lokacin da watan Ramadana ya ke zuwa karshe.

Wasu da aka fitar da su daga gidajen yarin a Kano sun bayyana irin yadda rayuwa take a gidan kason, abin da suka ce rayuwa ce mai matukar kunci.

"Ina ji na kamar wanda ya mutu aka ce ya shiga aljanna.Na ji dadi kuma Allah ya yaye wa wadanda muka bari a can," in ji wani mutum da aka ceto.