Kim Jong-un ya kashe mai kula da kunkuru

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan ba shi bane karo na farko da wannan shugaban yake hallaka jami'ansa ba

Rahotanni daga Korea ta Arewa na cewa an kashe manajan gidan wata gona da ake kiwon kunkuru sakamakon wata ziyara da shugaban Kasar Kim Jong- un ya kai gidan gonar cikin watan Mayu.

Wata kafarwatsa labaran kasar ta ce -- a lokacin ziyarar -- shugaban ya soki ma'aikatan gidan gonar da ke kan kogin Taedong da yin sakaci wajen mutuwar daruruwan kunkuru sababbin kyankasa.

Manajan gidan gonar kiwon kunkurun ya ce yawan daukewa wutar lantarkin ne ya kawo cikas ga kokarin da ake yi na tara ruwa a tankunan da kunkurun ke ciki.

Masu aiko da rahotanni sun ce jami'an Koriya ta Arewa na fuskantar hatsarin harbewa idan suka ja da dokokin Kim Jong- un wanda a lokuta da dama ya kan ziyarci ma'aikatu domin duba wuraren da ake gudanar da aiki.

Ana amfani da naman kunkuru wajen yin miya a kasar.