Microsoft zai kori ma'aikata 8,000

Hakkin mallakar hoto Stephen Brashear. Getty. Microsoft
Image caption A bara Microsoft ya sayi kamfanin Nokia

Katafaren kamfanin nan na Microsoft mai yin manhajar kwamfuta ya bayyana wani zagayen na babban zabtare yawan ma'aikatansa.

Zai sallami ma'aikata kusan dubu takwas, galibinsu a bangaren waya Nokia, da microsft ya siya a bara.

Haka kuma kamfanin na Microsoft ya zabtare darajar sashen wayar, wanda ya saya dala fiye da biliyan bakwai.

Wayoyin Microsoft Windows dai na fadi tashin yin gogayya da jagororin kasuwa, Android da iPhone.