Shugabannin Amurka da Vietnam sun tattauna

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Obama da Mista Nguyen Trong

Shugaban Amurka Barrack Obama ya yi wata ganawa a fadar White House da shugaban jam'iyyar kwamunisanci na kasar Vietnam, Nguyen Phu Trong.

Wannan shi ne karo na farko da Amurkan ta gudanar da irin wannan tattaunawa tun bayan da kasashen biyu suka gyara dangantaka a tsakanin su shekaru 20 da suka gabata.

Shugaba Obama ya ce kasashen biyu suna kara karfafa hadin kai a tsakanin su duk da banbancin tsarin siyasar su da kuma abinda ya kira tarihin su mara dadi.

A wannan watan ne a ke cika shekaru 40 da kawo karshen yakin Vietnam.

Amurka na tana duba yiwuwar kulla wata babbar yarjejeniyar kasuwanci da Vietnam da sauran kasashe kawayenta a nahiyar Asiya a wani yunkuri na samun kasuwanni da kuma rage karfin China a yankin.

Masu zanga zanga sun tattaru a wajen fadar ta White House suna kiran a inganta sha'anin kare hakkin bil'adama a Vietnam.