An gano maganin da ke rage cutar dajin nono

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masana kimiyya sun gano wani maganin lafiya mai rahusa wanda ke taimakawa mata masu ciwon daji a nono.

Masana kimiyya sun gano wani maganin lafiya mai rahusa mara hadari wanda ke taimakawa mata masu ciwon daji a nono.

Binciken da suka yi, wanda aka wallafa a wata mujalla mai suna 'Nature', wanda basu kammala ba, amma ya yi nuni da cewa za a iya amfani da wani sinadari, watau Progesterone domin a tsayar da yaduwar cutar dajin.

Masu binciken a kasashen Biritaniya da Australia sun ce sakamakon binciken na da fa'ida sosai, kuma suna shirin gwaji a asibitoci.

Hukumar bincike a kan ciwon daji ta ce binciken yana da muhimmanci kuma zai iya taimakawa dubban mata.

Kwayoyin halitta na da nasaba kwarai a ciwon daji na nono.

Bincike a dakin gwaje-gwaje ya nuna cewa kwayoyin halitta suna kara girma idan aka saka masu sinadarin Progesterone da Tamoxifen, fiye da idan an saka masu Tamoxifen kawai.

'Rage yaduwa'

Daya daga cikin masu binciken, Farfesa Carlos Caldas daga Jami'ar Cambridge, ya shaidawa BBC cewa, "Da alama za a iya dakile cutar ta haka, amma in har za a gane ko zai fi maganin ciwon dajin nono a mata, toh sai an yi gwaji."

Masu binciken na cikin matakin farko domin gudanar da gwajin maganin a asibiti.

Kusan kaso 75 cikin 100 na mata masu cutar dajin nono na da cutar mai nau'in Oestrogen, kuma cikin su kaso 75 cikin 100 na da cutar mai nau'in Progesterone.

Ana saran rabin kason mata da ke fama da cutar, za su amfana da wannan shiri.

Dr. Emma Smith wacce ke cibiyar bincike a kan cututtukar daji ta Biritaniya, ta ce sakamakon da ake samu tun yanzu na nuna alamun nasara.

Likitar ta shaidawa BBC cewa "Wannan sakamakon da aka samu yana da muhimmanci sosai. Zai iya kasancewa hanya mara tsada, kuma mai sauki na samun lafiyar dubban mata, amma ana bukatar gwaji a asibiti."