Ana zanga-zanga a Ghana

Image caption Masu zanga-zanga a Ghana

Ma'aikata suna zanga-zanga a garin Tema da ke Ghana a kan tsadar rayuwa da kuma almubazarrancin gwamanti.

Kungiyar masu masana'antu ta shirya zanga-zangar ce a yayin da ake fuskantar hauhawar farashin man fetur da wutan lantarki kuma darajar kudin kasar 'cedi' tana faduwa, lamarin da ke shafar kudaden kayayyakin da ake shigowa da su kasar.

Wakilin BBC -- wanda ya dauki wadannan hotunan - ya ce ma'aikata suna dauke da gunkin akuya, wanda hakan wani shagube ne na kalaman da shugaban Ghana ya yi cewa yana fama da matsalar matacciyar akuya idan ma'aikata na zanga-zanga, inda yake nufin ba zai saurari duk wani korafi na ma'aikata ba.

Tema shi ne garin tashar jiragen ruwa wanda ke yankin Greater Accra.

Yana da nisan kilomita 25 daga Accra, babban birnin Ghana.