Sheikh Aminuddeen Abubakar ya rasu

Hakkin mallakar hoto AFRICA TV
Image caption Sheikh Aminuddeed ya rasu yana da shekaru 69 a duniya kuma ya bar 'ya'ya 18.

Shahararren malamin addinin musulincin nan na Kano, Sheikh Aminuddeen Abubakar ya rasu.

Bayanai sun nuna cewar malamin ya rasu ne a kasar Saudiyya.

Kafin rasuwar sa dai malamin shi ne babban limamin masallacin Da'awah da ke kano.

Sheikh Aminuddeen Abubakar ya rasu ne yana da shekaru 69 a duniya kuma ya bar 'ya'ya 18.

Ana sa ran za a yi jana'izar sa idan an jima.

Allah ya jikan sa da gafara, ameen.