'Yan gudun hijirar Syria sun haura 4m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa yanzu, adadin mutanen da suka tsere daga Syria ya haura miliyan hudu.

Akasarin su sun gudu zuwa makwabtan kasashe da suka hada da Jordan da Lebanon da Turkiya.

Wasu 'yan kasar ta Syria sun gudu ne zuwa Iraki duk da sabon tashin hankali da Irakin ke fuskanta.

Fiye da mutane miliyan bakwai ne suka rasa matsugunnansu a Syria, yayin da rabin mutanen kasar suka bar gidajensu na ainihi tun bayan barkewar fadace-fadace a shekarar 2011.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan shi ne lamarin 'yan gudun hijira mafi girma a shekaru masu yawa, sannan ta yi gargadin tana sa ran adadin ya haura haka a watanni masu zuwa.