Jiragen sama sun koma zirga-zirga a Maiduguri

Image caption Filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos

Jiragen sama na 'yan kasuwa sun koma zirga-zirga zuwa Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kamfanin Jiragen sama na Medview, wanda ke dauke da fasinjoji sama da dari, shi ne jirgin sama na farko da ya isa jihar a ranar juma'a da rana.

Jirgin ya taso ne daga filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Lagos.

Jirgin sama na Medview zai rika tashi zuwa Maiduguri sau hudu a kowanne mako.

An dai rufe filin jirgin saman na Maiduguri ne watanni 18 da suka wuce, saboda rikicin Boko Haram.

Birnin Maiduguri shi ne cibiyar kasuwanci ce a arewa maso gabashin Najeriya, kafin hare-haren kungiyar ta Boko Haram.