Ma'aikatan mai 12 sun rasu mutu a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba a san abin da ya janyo fashewar ba

Kamfanin mai na kasar Italia, Eni, ya bayyana cewa wasu mutane goma sha biyu sun rasa rayukansu a lokacin da suke aiki a reshen kamfanin da ke yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a Nigeria.

Kamfanin ya ce ma'aikatan suna gudanar da wasu gyare-gyare ne a lokacin da abun ya faru.

Haka nan kuma wasu mutane uku sun samu raunuka.

Kamfanin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Kamfanin Eni din ya kara da cewar an soma bincike kan abin da ya janyo fashewar.