An daure mutumin da yayi wa Madonna kutse

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mawakiya Madonna

Mahukunta a Tel Aviv sun yanke wa wani mutumin Isra'ila hukuncin daurin watanni 14 a gidan yari saboda ya yi wa mawakiyar nan Madonna kuste a cikin kwamfutar ta.

An kama Adi Lederman mai shekaru 39 ne a watan Janairu, bayan wani bincike da hukumar FBI ta taimaka aka gudanar.

A wani yunkuri na sasantawa a wajen kotu, Mista Lederman ya amsa laifin yin kusten da keta hakkin mawakiyar na sirri.

Kusten ya tilasta ma Madonna fitar da wasu wakoki shida saboda an riga an sanya su a intanet a watan Disamba.

Mista Lederman wanda aka ci shi tarar dala 2600, ya taba shiga gasar nuna hazaka ta Isra'ila kwatankwacin American Idol, kafin daga baya a fitar da shi a gasar.

Kotun data yanke mushi hukunci ta ce Mista Lederman yana da matsala ta rashin lafiya, lamarin da yasa aka mushi sassauci a hukuncin.