Kotu ta ba da belin Nyako

Image caption Ana zargin tsohon gwamnan da wawure dukiyar al'umma

Wata babbar kotu da ke Abuja a Nigeria ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da dansa Sanata Abdul'aziz Nyako wadanda ke fuskantar tuhumar almundahana da kudaden gwamnati.

A zaman da ta yi, kotun ta kuma bayar da belin wasu mutane biyu da ke fuskantar shari'a tare da tsohon gwamnan.

Wannan ya biyo bayan amincewa da alkalin kotun ya yi da bukatar neman belin da lauyoyin da ke kare suka gabatar bisa hujjar cewa laifukan da ake zarginsu wadanda doka ta yarda a bayar da beli ne.

Alkalin kotun Justice Evoh Stephen Chukwu ya dage sauraren shara'ar har zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

A cikin wannan makon ne hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasar zagon-kasa ce ta gurfanar da su a gaban kotun.