Masu kunar bakin-wake 'yan wuta ne - Sheik Alasan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin Jos ya fuskanci hare-haren ta'addanci a baya bayan nan

Wani malamin addinin musulunci a Jos, babban birnin jihar Plateau da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, Sheikh Alasan Sa'idu Jos, ya ce duk wanda ya yi harin kunar-bakin wake to wuta ce makomarsa.

Da ya ke tsokaci dangane da masu da'awar jihadi ta hanyar kai hare-haren kunar bakin-wake a kan mutane, a cikin shirin BBC na Ra'ayi Riga da aka gabatar ranar Juma'a, Sheikh Alasan ya ce ba bu wani wuri da addinin musulunci ya ba da dama ga wani da ya kashe kansa har ma ya kashe wasu.

Ya bayyana al'amarin da jahilci wanda ya ce yana faruwa ne sakamakon karanta litattafai da masu irin wannan akida suke yi ba tare da sun je gaban malaman ilimi ba.

Ya kuma kara da kwatanta masu irin wannan akida da jakai dauke da damman litattafai.

A daren ranar Lahadi ne dai wasu da ake kautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai tagwayen hare-haren bama-bamai a kan wani gidan abinci da masallaci.

Al'amarin kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 50 sannan wasu da dama sun jikkata.