'Yan Biritaniya zasu fice daga Tunisia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu yawon bude ido a bakin tekun 'yan hutu a Tunisia.

Dubban masu yawon bude ido na shirin barin kasar Tunisia, yayin da gwamnatin Biritaniya tayi gargadin cewa ana tunanin 'yan ta'adda za su sake kai musu hari.

Kungiyar kamfanonin shirya yawon bude ido na Biritaniya, ta dauki aniyar mayar da abokan huldar ta gida cikin sa'o'i 48.

'Yan ta'adda masu ikirarin jihadi, sun hallaka masu yawon shakatawa 38 a bakin tekun kasar, wadanda yawancin su 'yan asalin Biritaniya ne a watan da ya gabata.

Gwamnatin Biritaniya ta ce tsaro da aka tsaurara tun a wancan lokacin ba zai isa ba.

Jakadan Tunisia a Biritaniya, Nabil Ammar ya zargi kasashen Turai da biye wa 'yan ta'addan.

Akalla yawan 'yan yawon bude ido 2500 zuwa 3000 daga Biritaniya ke zuwa kasar Tunisia ta hanyar kamfanonin, matafiya masu zaman kansu kuma za su kai 300.