Ebola: Za a bayar da karin tallafi

Hakkin mallakar hoto AP

Masu bayar da tallafi a taron majalisar dinkin duniya da akayi a New York sun yi alkawarin bayar da dala biliyan 3 da miliyan dubu dari 4 ga kasashen yammacin Afrika uku da ke fama da cutar Ebola.

Masu bayar da tallafin sun ce za su bayar da kudaden ne domin a samu damar shawo kan cutar a kasashen.

Shugabar shirin raya kasashe ta majalisar dinkin duniya Helen Clark ta kira wannan yunkuri a matsayin abin da ya dace.

Cutar ta Ebola wacce ta bulla a karshen shekarar 2013, ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da dubu goma 11 a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban- ki Moon ya ce har yanzu akwai bukatar taimakon kasashen duniya wajen yaki da cutar.