Fararen hula 12 bam ya kashe a Afghanistan

Harin bam a Afghanistan Hakkin mallakar hoto
Image caption Harin bam a Afghanistan

Jami'an tsaro a kasar Afghanistan sun ce fararen hula akalla goma sha biyu ne aka kashe a wasu hare-haren bam da suka faru a wurare biyu.

Wani babban jami'in 'yansanda a gabashin lardin Kapisa ya ce fararen hula 10 ne suka hallaka, yayinda mutane 7 suka samu raunuka, lokacin da wata motar da suke ciki ta ci karo da wani bam a bakin hanya.

A arewacin lardin Kunduz kuma, fararen hula biyu ne suka mutu lokacin da wani bam din na bakin hanya ya fashe kusa da wata motar 'yansanda dake wucewa.

Babu dai wata kungiyar da ta fito tayi ikirarin kaddamar da harin, amma kuma kungiyar mayakan Taliban ce aka fi sani da kai hare-hare a duka yankunan biyu.