Mabarata za su kai jihar Kaduna kotu

Image caption Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i

Mabarata akasari nakasassu, a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun yi barazanar gurfanar da gwamnatin jihar a gaban kuliya bisa hana su bara da kuma yi wa 'ya'yansu kazafin ta'addanci.

A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya sanar da dokar hana barace-barace da saye da sayarwa a kan titunan jihar.

Hakan ya biyo bayan harin bom da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 20 a sakariyar karamar hukumar Sabon Gari, a Zariya.

Kuma gwamnatin na cewa ta kafa wannan doka ne domin kare dukiya da rayukan jama'a.

To sai dai mabaratan sun gudanar da wata zanga-zanga domin nuna fushinsu bisa dokar, suna kuma fadin cewa an hana su hanyar neman abinci ne ba tare da an sama mu su wata mafita ba.

Sun kuma ce an yi musu wani kazafi mai zafi bisa cewa a na amfani da 'ya'yansu wajen kai hare-haren kunar-bakin wake.

Yanzu haka sun deba wa gwamnatin kwana uku kacal da ta janye dokar da kuma kazafin ko kuma su gurfanar da ita a gaban kuliya manta sabo.