An kai hari gidan yari a jihar Diffa

Wani hari da Boko Haram suka kai a jamhuriyar Nijar. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram sun fadada kai hare-haren su zuwa kassahen da ke makoftaka da Nigeria, ciki har da Jamhuriyar Nijer.

Rahotanni daga jihar Diffa mai iyaka da Nigeria na cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a gidan yarin garin, a cikin daren jiya.

An dai yi gumurzun tsakaninsu da jami'an tsaro, inda jami'an sukai nasarar hallaka maharan 3, an kuma yi hasarar wani Kyaftin din sojin Nijar guda daya.

Mazauna jihar Diffa sun shaidawa BBC cewa maharan sun yi shigar burtu ne, inda suka sanya kakin sojin kasar Chadi a wata dabara ta shiga gidan yarin ba tare da sun samu turjiya ba.

Daman mazauna Diffa sun ce an dauki kwanaki ana ganin mutanen masu sanye da kakin sojin, kuma ba su kawo komai a ran su ba ko zargin ba sojojin Chadi ba ne.

A yanzu dai kura ta lafa, mutane sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.