Buhari ya kori manyan jami'an tsaro

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari a lokacin taro da hafsoshin tsaron

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sallami manyan jami'an tsaron kasar.

Shugaba Buhari ya kori hafsan hafsonshin rundunar sojin sama da ta kasa da ta ruwa.

Wadanda aka kora su ne: Air Marshal Alex Badeh, Janar Kenneth Minima da Rear Admiral Usman Jibrin da kuma Air Vice Marshal Adesola Amosun.

Wata majiya a fadar shugaban Nigeria ta shaida wa BBC cewar nan gaba a ranar Litinin za a sanar da sabobbin manyan hafsoshin tsaron.

An dade ana saran shugaba Buhari zai kori manyan hafsoshin tsaron a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a cikin kasar.

A cikin kwanaki goma da suka wuce an kashe mutane fiye da 220 a Nigeria sakamakon hare-haren Boko Haram.

Tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ne ya nada su.