Chadi ta mayar da 'yan gudun hijira 300 Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin 'yan gudun hijira 300 ne Chadi ta dawo da su Najeriya

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta tabbatar da karbar 'yan gudun hijira kimanin 300 wadanda rikicin Boko Haram ya tilastawa ketarawa zuwa kasar Chadi.

Rahotanni dai na cewa kasar ta Chadi ta mayar da 'yan Najeriyar masu neman mafaka a yankinta ne saboda yawan da suka yi mata.

Alhaji Mohammed Kanar, wakilin hukumar ta NEMA mai kula da yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa akasarin mutanen da aka mayar da su 'yan jihar Borno ne kuma dukkannin su suna cikin koshin lafiya.

Ya kara da cewa hukumar ta nema ta tarbi mutanen a sansaninta kuma za a mayar da su garuruwansu idan har akwai yiwuwar hakan.

Rahotanni sun ce ko a watan Mayun 2015 ma, Jamhuriyar Nijar -- wadda makwabciyar Najeriyar -- ta mayar da 'yan Najeriya sama da dubu uku masu neman tsira a cikin kasar a wani mataki na hana yaduwar Boko Haram a kasar.