Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane mini hanya 11/07/15

Najeriya na daga cikin kasashen da suka fuskanci karayar arziki sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Kuma wannan ne ya sa gwamnatin kasar ke duba hanyoyin fadada kafofin samun kudin-shigarta maimakon dogaro ga mai.

Masana da dama dai na ganin cewa babu zabin da ya fi komawa ga sana'ar noma da kiwo, wadanda a baya suka rike kasar, duk kuwa da dimbin fama da matsalolin da suka fama da su, ciki har da matsalar rashin kayan aiki, da satar dabbobi da kuma kararar hamada.

Dr Abubakar Sulaiman, dalibi ne da ke karatun digirin-digirgir a Kwalejin ayyukan Noma da kula da lafiyar dabbobi ta Royal Veterinary College da ke London, kuma a tattaunawa ta musamman da suka yi da Ibrahim Isa, ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari za ta iya bunkasa harkar noma idan ta yi kyakkyawan tsari ta kuma aiwatar ka-in-da-na-in.