Me yasa aka rarraba hoton Makkah?

Hakkin mallakar hoto Getty

Kusan mutane dubu 300,000 ne su ka aika sako ta tweeter da maudu'in #mecca_live a wani bangare na kamfe na nuna Saudiyya a shafin sada zumunta na "snapchat", wanda ba a bari wadanda ba Musulmai ba su shiga.

A shekarar da ta wuce ne Snapchat ya kaddamar da wani dandali da zai rika bayar da bayanai kai-tsaye.

Dandalin yana bai wa masu amfani da shi damar aike wa da bidiyo da hotuna kai-tsaye, wadanda, kamar sauran bayanan da ke cikinsa, ke bacewa idan suka dan jima.

Yayinda snapchat ya ke mai da hankali a kan wurare da ya zaba -ciki hadda bidiyon abubuwan da suke faruwa a Tel aviv kai tsaye a makon da ya gabata, abin ya zama wani kamfe na kamun kafa- wanda ya hada kokari na baya bayan nan na abubuwan da ke wakana a garin Makkah a lokacin miliyoyin mutanensu ke yin sallah a cikin birnin.

'Takaitattacen bayani a kan Makkah'

A wurin Musulmai, Makkah shi ne wuri mafi tsarki a doron kasa.

A nan aka haifi Annabi Muhammad (S.A.W) kuma a nan ne aka yi masa wahayi na Al-qurani na farko.

A duk shekara, Musulmai daga sassa daban-daban na duniya suna tururuwa zuwa birnin Saudiyya domin yin aikin Hajj.

An bukaci Musulmai su yi aikin hajji a kalla sau daya a rayuwarsu idan har suna da hali da koshin lafiya.

Amma kuma wadanda ba za su iya yin aikin Hajji ba a lokacin Hajji, za su iya yin Umrah.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ana yawan yin Umrah a cikin watan Ramadan - wasu malamai addinin musuluncin suna da hujjar cewar yin Umrah lokacin watan Ramdan kwatankwacin yin aikin Hajji ne.

Mutane da dama daga cikin daruruwan dubban masu yin kamfe a nuna Makkah a manhajar Snapchat suna fatan daukar hotunan zai nuna kyawun aikin hajji.

Ga wadanda suke a waje, zai iya zama wata hanya mai ban sha'awa da za su ga abin da ba kowa ke iya gani ba - ba a barin wanda ba Musulmi ba su shiga birnin.

Wani dan kasar Saudiyya ya ce "Suna fada a ko da yaushe cewar ba a bacci a birnin New York. Basu ga Makkah ba tukuna.Muna so maudu'in #mecca_live don Allah."

'Gangami a watan Afrilu'

'Yan Saudiyya sun bukaci Snapchat ya dauki bidiyo kai tsaye na abubuwan da za su wakana a ranar 27 ga watan Ramadan kamar yadda aka yi amannar cewar yana daya daga cikin dare mafi albarka na watan.

Idan aka yi nasara a kamfe din, ba zai zamo karo na farko da aka nuna birnin Saudiyya a manhajar ba.

A watan Afrilun da ya gabata an samu wani shiri da ya kamata ya nuna yadda rayuwar 'yan kasar Saudiyya ta ke a birnin amma maimakon nuna hakan, shirin ya mai da hankali ne wajen nuna wasu abubuwa na batanci a kan yadda 'yan Saudiyyar su ke.

Hakan ya sa 'yan kasar Saudiyya sun nuna damuwa a kan cewar hakan za ta sake faruwa.

Wani ya saka a cikin shafinsa na twitter cewar 'yan uwana mazauna Makkah, idan aka wallafa wannan shafi dan Allah kada ku mai da shi wani abi na barkwanci.

Manhajar Snapchat bata ce komai ba a kan kamfe din a lokacinda BBC Trending ta tuntube su.

Hakkin mallakar hoto Getty