Kotu ta wanke wasu mata a Morocco

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hukuncin kotun nasara ce ga masu taya matan yakin neman 'yanci.

Wata kotu a kasar Morocco ta wanke wasu mata biyu da aka zarga da sanyan kaya na rashin da'a a cikin jama'a.

Lamarin ya janyo cece-ku-ce sosai a kasar.

Lauyan matan ya ce wannan hukunci da kotu ta yanke alamu ne na nasara ga su matan da kuma wadanda suka taya su yakin neman 'yanci.

Matan masu shekaru 23 da 29, masu aikin gyaran gashi ne kuma an kamu su ne a wata unguwa mai suna Agadir, suna hanyar zuwa wajen aikinsu.

Irin wannan laifi na iya janyo hukuncin daurin shekaru biyu a dokokin kasar ta Morocco.