Leicester City ta dauki koci Ranieri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranieri ya taba jan ragamar Chelsea

Leicester City ta nada Claudio Ranieri a matsayin sabon kociyanta kan kwantiragin shekaru uku.

Ranieri mai shekaru 63, zai maye gurbin Nigel Pearson wanda aka sallama a watan Yuni.

Pearson shi ne ya jagoranci Leicester buga gasar Premier a bara, kuma da kyar ta ci gaba da zama a gasar da aka kammala.

Ranieri dan kasar Italiya ya taba horas da Chelsea a Stamford Bridge a shekarar 2004.