Faduwar gini ta kashe sojin Rasha 23

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wakilin BBC a Moscow ya ce ana tsammani gyara maras inganci da aka yi wa ginin a shekarar da ta wuce ne ya yi sanadiyar faduwar ginin.

Wani bangare na ginin barikin sojin Rasha ya fadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 23.

Kazalika, an ceto sojoji 19 daga baraguzan ginin da ya rushe a kusa birnin Omsk na lardin Siberia.

Wani mutum da ya tsira ya shaida wa gidan talabijin na kasar cewa sojojin suna barci a lokacin da ginin ya rushe.

Wasu hotunan talabijin sun nuna yadda ginin mai hawa hudu ya rufta, sannan ya yi wani wawagegen rami, kuma soji sun kewaye shi domin kawar da baraguzan ginin.

Wakilin BBC a Moscow ya ce ana tsammani gyara maras inganci da aka yi wa ginin a shekarar da ta wuce ne ya yi sanadiyar faduwar sa.