Mutane na tserewa daga Damasak

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram ya raba mutane da muhallansu

Rahotani daga garin Damasak na jihar Borno a Nigeria na cewa kusan daukacin mazauna garin sun kwarara zuwa wasu yankuna na jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar.

Mutanen sun ce suna gudu ne saboda sojojin hadaka na Chadi da Nijar sun bayyana aniyarsu ta ficewa daga garin, bayan sun kwashe watanni suna gudanar da ayyukan tsaron.

"Sojoji sun ce za su tashi su bar wajen, muma shi ya sa muka gudu," in ji wani da ya bar Damasak.

Bayanai sun ce mutanen Damasak a yanzu suna neman mafaka a Masallatai a Diffa da wasu wuraren.

Garin Damasak na daga cikin garuruwan da 'yan Boko Haram ke iko kafin dakarun hadin gwiwa na Nijar da Chadi su kwato garin.