An hallaka mutane 43 a Monguno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da aka nada sabbin jami'an tsaro

Rahotanni daga Munguno a jihar Borno Nigeria na cewa a kalla mutane 43 ne aka kashe sakamakon wasu hare-hare 'yan Boko Haram.

An kaddamar da hare-haren ne a wasu kauyukan karamar hukumar Munguno guda uku, ranar Juma'ar da ta gabata.

Sai dai kuma labarin harin bai fito ba sai a ranar Litinin, ranar da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya nada sabobbin shugabannin tsaro na kasar.

An dai ce al'amarin ya faru ne a kauyen Kalwa da Misala da kuma Gollam dukkaninsu a yankin karamar hukumar Munguno.

Rahotannin sun ce maharan dai sun shiga garuruwan ne daren ranar Juma'ar, a inda kuma suka bude wa mutanen wuta, suka kuma yayyanka wasu, sannan daga bisani suka yi awon gaba da kayan abinci.