Tsipras na fuskantar tirjiya daga 'yan majalisa

Alexis Tsipras Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alexis Tsipras

Firaiministan kasar Girka, Alexis Tsipras zai tun kari majalisar dokokin kasar domin jan hankalinsu da su amince da sharuddan da aka gindaya wa Girkar kafin a kara ba ta tallafin da ya amince da shi yayin tattaunawarsa da shugabannin kungiyar kasashen turai jiya Litinin a Brussels.

Shugabannin turan sun bukaci majalisar dokokin kasar ta Girka da ta sanya sharuddan sabon ceton da za a ba wa kasar a jerin dokokin kasar daga nan zuwa ranar Laraba.

Sharuddan dai sun hada da kara kudin haraji da rage kudaden fansho. Sai dai wasu 'yan jam'iyyar ta firaiministan sun ce ba za su mara masa baya ba.

Ya ce jiya firaministanmu ya fuskanci wani abu kamar juyin mulki wanda kasar jamus da sauran kasashe kamar su Netherlands da finland da kuma Baltic ke kokarin su yaudare shi.

Ministan tsaron kasar ta Girka Panos Kammenos ya bayyana wadannan sharuda a matsayin juyin mulki.