'An cimma matsaya kan nukiliyar Iran'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A karkashin yarjejeniyar, Iran ba za ta bari masu sa ido kan makamashinta su duba shi kai-tsaye ba.

Jami'an diplomasiyya sun ce Iran ta amince ta takaita shirinta na samar da makamashin nukiliya, inda a waje daya kuma za a janye takunkumin da aka sanya mata.

An cimma yarjejeniyar ne a birnin Vienna na Austria.

A karkashin yarjejeniyar, masu sa idanu kan nukiliyar na Iran ba za su samu bayanai kai-tsaye ba.

Haka kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta ce ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da Iran kan makamashin nukiliyarta.

Kasashe shida da ke da karfin fada-a-ji a duniya, cikinsu har da Amurka da Rasha da Biritaniya sun kwashe shekara da shekaru suna ganawa da Iran kan makamashin nukiliyar nata.