Moses zai samu gurbin wasa a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victor Moses

Kocin Stoke City, Mark Hughes, y ace Victor Moses zai samu gurbin da zai dinga buga wa Chelsea wasanni a bana.

Moses mai shekaru 24, ya buga wa Stoke wasanni aro a Britannia a kakar bara.

Dan was an ya ci kwallaye hudu daga cikin wasanni 23 da ya buga wa Stoke City wasanni aro.

Stoke ta tuntubi Chelsea da ta sayar mata da dan kwallon a inda Chelsea ta ki amincewa da yin hakan.

Rabon da Moses ya buga wa Chelsea wasanni akai akai tun lokacin da Jose Mourinho ya karbi aikin horas da kungiyar shekaru biyu da suka wuce.

Chelsea ta yi musaya da Stoke, a inda Asmir Begovic ya koma Stamford Bridge, Marco van Ginkel zai taka leda aro a filin wasa na Britanniya.