Museveni na kokarin sasantawa a Burundi

Shugaban Uganda, Yuweri Museveni ya yi tattaki zuwa kasar Burundi domin shiga tsakanin wakilan jam'iyya mai mulkin kasar da kuma bangaren 'yan adawa.

Kasar Burundi dai ta fada rikici tun lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya kudiri aniyar yin ta-zarcen wa'adi mulki karo na uku a zaben da ake sa-ran yi a mako mai zuwa.

Sai dai shi ma shugaba Yuweri Museveni da ke yi wa kallon mai shiga tsakanin, a halin da ake ciki yana cin wa'adin mulkinsa ne karo na hudu, kuma ya shafe kusan shekara 30 yana mulkin Uganda.

Sama da mutane 70 ne aka halaka a kasar Burundi a cikin watanni biyun da suka wuce.

Tarayyar Turai da sauran kasashen Afrika duk sunyi Allawadai da yunkurin shugaban kasar na tsawaita wa'adin mulkinsa.