Mutane 20 sun mutu a taron addini a Indiya

Sama da mutane 20 sun mutu a jihar Andhra Pradesh ta Indiya sakamakon tirmutsitsi a wani bikin addinin Maha Pushkaralu.

Dubun-dubatar mabiya addinin ne suka taru a kogin Godavari domin yin wankan ibada.

'Yan sanda sun bayyana cewa mutanen sun mutu ne lokacin da wasu daga cikin dandazon jama'ar da ta taru suka yi ribibin kutsawa ta kofar shiga harabar Kogin.

An dai saba da ganin tirmutsitsi a Indiya a wasu taruka, inda gayyar jama'a kan yi rige-rigenkama wurin zama.