El-Rufai ya yi wa manyan sakatarori ritaya

Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption El-Rufai ya ce zai rage kashe kudaden gwamnati

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa manyan sakatarorin gwamnati su 20 ritaya.

Sanarwar da kakakin gwamnan, Samuel Aruwan ya sanyawa hannu ta ce gwamnan ya dauki matakin ne a ci gaba da yunkurinsa na rage yawan kudin gwamnati da ake kashewa.

Tuni gwamnan ya rage yawan ma'aikatu a jihar daga 19 suka koma 13.

El-Rufai ya ce ritayar da aka yi wa manyan sakatarorin, za ta ba da damar samun kudaden yin wasu ayyukan da suka hada da gina makarantu, da hanyoyi da kuma asibitoci.

Tun bayan da aka rantsar da shi, Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin ganin ya aiwatar da sauye-sauye a harkokin gwamnati ta yadda al'umma jihar za su gani a kasa.