An ta da jijiyar-wuya a majalisar Girka

An tayar da jijiyar-wuya a majalisar dokokin Girka, lokacin da 'yan majalisar ke tattaunawa a sauye-sauyen da hukumar kasashe masu amfani da kudin Euro ta bukaci kasar da yi.

Wasu 'yan kwamitin majalisar dokokin sun yi ta katse tsohon ministan kudin kasar, Yanis Varoufakis lokacin da ya yi kokarin kwatanta yarjejeniyar da kasar ta cimma da kasashen da ke bin ta bashi da yarjejeniyar Versailers.

Yarjejeniyar dai ta yi sanadin ladabtar da kasar Jamus a karshen yakin duniya na farko.

Ana dai sa ran 'yan majalisar za su tabka muhawara a kan sauye-sauyen kafin su amince da yarjejeniyar da aka cimma da kasashe masu bin Girka bashi.

Firayim Ministan kasar, Alexis Tsipras ya bukaci 'yan majalisar su goyi bayan yarjejeniyar, duk kuwa da cewa ba ta masa dadi ba.