'Yan majalisar dokokin Rwanda sun goyi bayan tazarce

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kagame na son yin tazarce a Rwanda

Majalisar dokokin Ruwanda ta amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran-fuska da nufin share hanya ga shugaban kasar, Paul Kagame da zai ba shi damar neman wa'adin mulki karo na uku.

Masu rajin kare hakkin bil'adama dai na zargin shugaban kasar da yi wa 'yan adawa kisan-mummuke, tare da takura kafafen yada labarai ta hanyar su sakewa.

Batun neman wa'adin mulki karo na uku da wasu shugabannin ke yi a Afrika na neman zama ruwan dare a nahiyar.

Wasu masana harkokin diplomasiyya na ganin hakan ba ya rasa nasaba da kwadayin da 'yan majalisar dokoki suke da shi a kasashen Afirka.