An kara shekarun aure a Spain

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firai ministan Spain Mariano Rajoy

Mahakunta a kasar Spaniya sun kara adadin shekarun da 'ya mace za ta cika kafin ta kai munzalin aure a kasar a shara'ance.

Yanzu an kara shekarun daga 14 zuwa 16 kafin 'ya mace ta samu amincewar Alkali, a daura mata aure.

Sai dai ba sosai al'umar kasar ke bin wannan doka sau-da-kafa ba, saboda a bara ma aure biyar kadai aka daura ta wannan hanyar.

An kafa sabuwar dokar ne da nufin hana auren-dole da kuma wasu mutane da bata kananan yara.