'Kamfanonin katako na rura rikicin CAR'

Image caption Sojojin gwamnati a Jamhoriyar Afrika ta Tsakiya

Kungiyar Global Witness ta zargi wasu kamfanonin yanka katako na Turai da taimakawa a yakin da ake yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kudade, ta hanyar cimma wata yarjejeniyar kasuwanci mai tsoka da kungiyoyin da ke dauke da makamai.

Kungiyar ta ce ta gano wasu 'yan kasuwa daga kasashen Faransa da Jamus da China da Labanon wadanda suke biyan miliyoyin daloli ga 'yan tawayen Musulmi da kuma Kirista.

A wani sabon rahoto da ta fitar, kungiyar ta zargi Tarayyar Turai da gazawa wajen dakatar da haramtaccen cinikin itatuwa a yankin Turai.

Rahotanni sun ce 'yan tawaye a Afirka ta Tsakiya na samun kudadensu ne ta wannan harka, abin da ke rura wutar rikicin.

Dubban mutane aka kashe a 'yan shekarun da suka gabata a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a wani rikici da ya haddasa kakkabe al'ummar musulmi 'yan tsiraru.