An fatattaki 'yan tawaye daga birnin Aden

Yemen

Mayakan sa-kai a Yaman tare da taimakon jiragen yakin Saudiyya sun fattaki 'yan tawayen Houthi a kusan dukkannin birnin Aden.

An kai hare-haren ne domin taimaka wa shugaban kasar da ke gudun hijira.

Ko shakka babu wannan ita ce komabaya mafi muni da 'yan tawayen Houthin suka samu, tun bayan da kasar Sa'udiyya ta fara kai hari ta sama a watan Maris a kan 'yan Huthin don goyon bayan Shugaba Hadi.

Nasarar da dakarun da ke goyon bayan Shugaba Hadin, wadanda ke yaki ta kasa suka samu a kan 'yan tawayen a wannan hari na baya-bayan nan, ya samu ne saboda sabbin makaman da suka samu daga kasashen yankin tekun Pasha da ke mara masu baya.

Kana sun kara samun dauki daga wasu dakarun da Sa'udiyya ta horas.

Haka kuma kawacen da Sa'udiyyar ke jagoranta sun yi aiki tare irin yadda ya kamata wajen kai hare-haren ta sama.

An dai kwace filin jirgin sama daga hannun 'yan Houthin, an kuma kwace galibin tashar ruwa da sauran yankuna masu muhimmanci sosai na birnin.

Sai dai akwai sauran fagagen daga masu yawa a Yaman din.