Bush ya karya kashin wuyansa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A keken guragu ake tura George Bush

An kwantar da tsohon shugaban Amurka, George HW Bush a asibiti bayan da ya karya wani kashi a wuyarsa sakamakon faduwar da ya yi a gidansa da ke Maine.

Kakakinsa ya ce ya na samun sauki kuma ba a saran zai dade kwance a asibiti.

Mr Bush wanda ke fama da rashin lafiya, ba ya iya amfani da kafafunsa kuma a bara ne ya cika shekaru 90 a duniya.

A karshen shekarar da ta wuce an kwantar da shi a asibiti saboda matsalar nunfashi.

Kakakin Mr Bush, Jim McGrath ya ce tsohon shugaban wanda shi ne mafi shekaru a tsakanin tsofaffin shugabannin Amurka hudu da ke da rai, ya ce dattijon zai dinga saka wani makari a wuyarsa sakamakon wannan raunin.