China ta hana fitar da man fetur daga Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin man Soraz wanda ke Zinder a Nijar

Kamfanin man fetur na kasar China (CNPC) ya hana fitar da man fetur na kamfanin Soraz daga Nijar zuwa kasashen waje.

Wani jami'in kungiyar ma'aikatan man fetur a Nijar, Boukar Elemi ya ce 'yan China sun dakatar da fitar da man fetur din Nijar zuwa ketare.

A bisa tsari dai, kamfanin Sonidep na Nijar ne ke lura da fitar da man fetur din kasar zuwa kasashen ketare.

Kawo yanzu hukumomin Nijar da kamfanin CNPC ba su ce komai ba a kan batun.

A shekara ta 2011 ne aka soma hako danyen mai a Nijar, inda matatar mai ta Soraz ke sarrafa ganga 20,000 na mai a kullum.

Ana amfani da kusan rabin man da ake hakowa ne a cikin kasarta Nijar sannan a sayar da sauran rabin a kasashen ketare.