Sojojin Japan sun soma shiryawa China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Japan ta ce ta na fuskantar kalubale daga China

Majalisar wakilan Japan ta amince da kudurin dokar da ya janyo cece kuce, wanda zai bai wa dakarun kasar damar fafatawa a wajen kasar a karon farko tun lokacin yakin duniya na biyu.

Firai Ministan kasar Shinzo Abe ne ya kirkiro da wadannan sauye sauye, wanda ya ce za su bai wa Japan din damar tunkarar sabbin kalubalan da take fuskanta musamman daga China.

Amma masu adawa da sauye sauyen sun ce sauye sauyen sun saba tsarin mulkin da ake amfani da shi bayan yakin Japan.

Gwamnatin Japan ce ke da mafi-rinjayen mambobi a majalisar wakilan kasar, sannan kuma jam'iyyun adawa sun kauracewa kuri'ar da aka kada.

Wannan sabon kudurin doka dai na fuskantar adawa daga galibin Japanawa