Wayar salular Samsung mafi sirintaka

Image caption Wayar Samsung Galaxy A8

Kamfanin latironik na Samsung ya sanar da wayar salular komai-da-ruwan-ka mafi sirintaka da ya kera.

Wayar Samsung Galaxy A8 mai kaurin 5.9mm, ta kasance siririya da kasa da kashi 85 cikin dari idan aka kwatanta da wayar Samsung da ta fi ko wacce tsada a yanzu, Galaxy S6 Edge.

Duk da sirintakar Galaxy A8, Injiniyoyin kamfanin Samsung sun yi kokarin kera mata batiri mai karfin 3,050mAh, da na'urar daukan hoto mai karfin 16-megapixel.

Sai dai wani kwararre a sha'anin fasaha ya soki alfanun kera wayar siririya.

A yanzu dai, kamfanin Samsung ya ce a China da Singapore ne kadai za a sayar da wayar Galaxy A8, amma ba za a kai ta Burtaniya ba.

Koda yake dai wannan shi ne karo na farko da kamfanin Samsung ya kera waya mai sirintakar haka, wasu kamfanonin kera wayoyin salula a China sun dade da kera wayoyin Android da suka fi Galaxy A8 sirintaka.

Wayar Vivo X5 Max ta fi Galaxy A8 sirintaka, domin ita kaurinta bai wuce 4.75mm ba. Ita ma wayar Oppo R5 kaurinta bai wuce 4.85mm ba, yayin da kaurin Gionee Elife S5.1 ya ke 5.1mm na ma'aunin kaurin wayoyi.

Daya daga cikin kalubalen kera wayar salula siririya kamar Galaxy A8 shi ne tsoron kada wayar ta rika lankwashewa a cikin aljihun mai ita.

Saboda wannan matsalar, kamfanin Samsung ya yi wa wayar sa gidan karfe domin ta kara karfi.