Shugaba Ghani ya jinjinawa Taliban

Image caption Shugaba Ashraf Ghani

Shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan, ya mika godiyarsa ga shugaban kungiyar Taliban Mullah Omar, wanda ya amince da sharuddan sasantawa tsakanin kungiyar da gwamnati.

A lokacin da yake jawabin Sallar Idi, Mr Ghani ya ce sakon da Mullah Omar ya sanar a cikin makonnan nan na daga cikin sakonnin zaman lafiya a kasar.

Ya kuma ce mayakan Taliban sun banbanta da sauran kungiyoyin 'yan tawaye da suke son shiga batun sasantawar.

Duk da wannan sako da Mullah Omar ya sanar, ana ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar, ciki har da wani bam da aka sanya a bakin hanya da yayi sanadiyyar rasa rayukan 'yan sanda biyar a kasar ta Afghanistan.

Sai dai babu wata kungiya da ta yi dauki alhakin kai harin.