Musulmai na bikin karamar Sallah

Image caption Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi a ranar Idi

Al'ummar Musulmi a kasashen duniya da dama suna bikin Eid al-Fitr ko kuma karamar Sallah bayan kamalla azumin watan Ramadana.

Musulmai kusan biliyan daya da dubu dari biyu ne suke gudanar da bukukuwan Sallar.

Eid al-Fitr na daga cikin bukukuwan ibada mafi girma a tsakanin al'ummar Musulmi.

Musulmi sun shafe kwanaki 29 suna gudanar da azumin watan Ramadana ba tare da cin abinci ba har sai rana ta fadi.

Sannan lokaci ne na ayyukan ibada domin kusanci ga Allah ubangiji.

Sai dai ana bukukuwan ne a lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro a kasashen Musulmi da dama ciki hadda Nigeria da Syria da Yemen da Somalia da wasu kasashen gabas ta tsakiya.