An yi jana'izar mutane 50 a Gombe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane

A jihar Gombe da ke arewacin Nigeria ana zaman makoki yayinda aka yi jana'izar dimbin mutane da suka rasa rayukansu a tashin wasu bama-bamai guda biyu.

Mutane a kalla hamsin ne suka rasu sannan wasu kimanin saba'in suka jikkata a birnin Gombe sakamakon tashin bama-baman a babbar kasuwar garin.

Wani wanda 'yan-uwansa na cikin wadanda aka yi wa jana'izar, Malam Muhammad Babangida, ya shaida wa BBC cewa an an yi Sallar jana'izar ce rukuni-rukuni ga mamatan.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Gombe, DSP Fwaje Attajiri ya tabbatar da cewa mutane hamsin ne suka mutu, wasu saba'in da suka jikkata a sanadiyar tashin tagwayen bama-baman a babbar kasuwa Gomben.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a arewacin Nigeria.